Zaffaffan Hotunan Rahama Sadau

590

Rahama ibrahim sadau dai Jaruma ce a Masana’antar Shirya Fina Finai ta kannywood, wacce ta zo masana’antat A shekarar 2013.

An haifi rahama dai a watan Satumba na 1993 a Jihar kaduna, ta kuma rayu Da iyayen ta na tsawon Rayuwar ta.

Ta fara karatun ta a gida Har zuwa Polytechnic inda ta karanta Business Administration a Kaduna Polytechnic.

Daga bisani ta matsa Zuwa Eastern Cyprus ta kanaranta Human resource management.

Bayan ta gama ta dawo ta ta bude wani gidan abinci mai auna “sadauz Home”.

Sadau dai Jaruma ce wacce bata bukatar wani dogon Jawabi domin kowa ya santa a Arewacin Nigeria dama Nigeria baki daya, domin ba iya masana’antar Shirya Fina Finan Hausa ta Tsaya ba ta shiga Har Nollywood.

Idan kuwa muka zaffaffa zamucce tayi shura a duniya baki daya, domin zamuga tana da ‘kawa wacce duniya ta santa wato Priyanka Choprar.

Yau dai kam a game da Batun kyau fa ba zancce komai ba Saboda yau Alkallancin Na ku ne ba nawa ba ne.

Idan kukayi Alkalancin sai nima nayi anfani dashi wajen sake bada Labari a gaba a kan Jarumar.

Jarumar dai zamu iya cewa Ta samu Shiga Masana’antar ne da ta Hadu da sarkin Masana’antar wato Jarumi Ali Nuhu.

Fim din Farko da ta Fara yi Shi ne Gani Ga wane a shekarar 2013.

Leave A Reply

Your email address will not be published.