Yadda zaka samu 2gb data a 200 kacal

6

Jama’a maziyarta shafin arewaclass barkanku da wannan lokaci.

A cikin wannan rubutu nawa zanyi muku dan takaitaccen bayani akan yadda zaku iya more garabasar data mai yawa akan kudi kalilan a layin airtel.

A shekarun baya mun kasance muna morar garabasar yin browsing kyauta a layukan wayoyinmu.

Amma daga baya sai wannan dama tayin browsing kyauta tayi karanci sakamakon yanda kamfanonin layukan suka matse hannayen su sosai.

Wannan rubutu nawa na kunshe da
bayani ne kan yadda zaka samu 2GB akan N100 ko kuma 10GB akan N500 kacal a layin ka na waya.

Abin farin ciki shine zaka iya amfani da wannan data wajen yin browsing akan ko wacce irin na’ura(karamar waya, kwamfyuta, Android, iPhone ds.. ).

Matakan da zaka bi wajen more wannan garabasa Matakan da zaka bi wajen cimma wannan bukata ba wasu masu yawa bane. Abinda ake bukata shine zakayi porting na layinka na wani network misali MTN zuwa airtel.

Mene ne porting?

Port na layi na nufin juyar da akalar
wani layi zuwa wani ba tare da
canzawar lambar waya ba.

Misali, juyar da layin MTN zuwa airtel ta yanda zai koma kamar layin airtel kuma mutum zai iya more duk garabasar da masu airtel ke mora.

Yadda Ake port din layi

Da farko dai ya kasance kana da layi
mai register (MTN ko Glo ko 9mobile da sauransu) Sannan sai ya kasance kana da ID card (National ID card ko voter card da
sauran su) Sai kaje ofishin airtel mafi kusa dakai kace musu kazo kayi port din layin kane, inda zasu bukaci wadancan abubuwan dana zayyano a sama.

Zasu baka form ka cike daga nan zaka ji anyo maka sako a layin da kake son porting din.

Inda daga bisani za’a bukaci ka kashe wayarka sannan ka
kunna(reboot).

Da zarar an kammala zaka ga network na MTN ya bace na airtel ya maye gurbin sa..

Yadda Zaka More Garabasar data ta 2GB akan N100 kacal Da zarar ka kammala porting layin yayi
lafiya lau. Sai kayi amfani da bank
recharge ko kuma zoto wallet wajen
sanya ma wannan layi naka katin kudi na N100.

Da zarar kayi hakan zasu turo
maka sakon cewa ka samu kyautar 2GB ta browsing.

Domin samun 10GB sai kai ta maimaita recharge din har sau hudu.

Don ka duba data balance naka sai ka danna *223# ko kuma *140#..

Wannan shine dan takaitaccen bayani akan yadda zaku iya more garabasar data ta 2GB ko 10GB a layin airtel.

©arewanobile

Leave A Reply

Your email address will not be published.