Wani Mutum ya karffawa Buhari Gwiwa yin tazarce

8

Mun samu labari cewa wani Jigo a Kudancin
Najeriya na Jam’iyyar APC Nyerere Anyim ya
nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya sake
tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.

An roki Shugaba Buhari ya fito takara a 2019
Nyerere Anyim wanda shi ya tsaya takarar
Gwamnan Jihar Abia a zaben 2015 yayi kira ga
Shugaban kasa Buhari ya zarce kurum domin
karasa ladan sa lokacin da yayi hira da gidan
Jaridar Daily Post a gidan sa.

Babban ‘Dan APC ya roki Shugaban kasar ya ji
kukan mafi yawan ‘Yan Najeriya da ke neman sa
ya kara fitowa zabe. Nyerere yace duk Najeriya
babu ‘Dan siyasar da zai iya doke Shugaban kasa
Buhari a zabe a Najeriya.

Wannan Babban ‘Dan siyasar kasar nan wanda
yana cikin manya a Gwamnatin Buhari ya ce
Shugaban kasar na bakin kokari kuma Jam’iyyar
APC tayi daidai na kara wa’adin Shugaban ta
John Oyegun yace yanzu 2019 ake hari.

©naij

Leave A Reply

Your email address will not be published.