Wani jigon kungiyar Bokoharam ya Shiga Hannu

0
A Ranar Talatar da ta gabata ne Rundunar Sojin Nigeriya ta sanar da cafke wani da ake zargin babban jigo ne a kungiyar Boko Haram mai suna Mohammed Mohammed Zauro a garin Damboa da ke jahar Borno. Rundunar ta bayyana cewa an kama mutumin ne a yayin da yake yunkurin tserewa daga dajin Sambisa zuwa Birnin-kebbi da ke jahar Kebbi. Haka kuma sanarwar ta ce sojojin sun kama wani dan Boko Haram din daban mai suna Lawal Aboi a tsakanin titin Damboa da Bale da ke jahar ta Borno. Sai dai Lawal ya yi ikirarin cewa da ma a kan hanyarsa yake na zuwa wajen sojojin domin ya mika wuyansa. Yanzu haka rundunar na kan binciken mutanen biyu. (143) via: Alummata.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.