Tab; wani saurayi ya mutu a gidan su budurwar sa

20

‘Yan sandan jihar katsina a arewacin Najeriya na tsare da wata budurwa da mahaifinta kan zargin kisan saurayin budurwar.

‘Yan sandan sun ce saurayin ya gamu da ajalinsa ne sakamakon wata takaddama da ta kaure kan
batun aure tsakaninsu da iyayen budurwarsa.

‘Yan sandan kuma suna tsare da wani makusanci ga saurayin budurwar.

Saurayin dai ya yanke jiki ne ya fadi a gidan su budurwar a garin Funtua bayan da mahaifin budurwar ya ce ba zai yadda ya aura ma sa ‘yarsa ba.

Saurayin Ma’aruf Yakubu dan shekara 22 kuma haifaffen garin shinkafi a jihar Zamfara.

Ana dai zargin budurwarsa Aisha ‘yar shekara 19 da zama sanadin mutuwarsa bayan ita da mahaifinta sun ce ba zai aure ta ba.

Yayin da shi kuma ya shaida wa mahaifin cewa budurwar na dauke da cikinsa.

A zantawar da na yi da Kanwar mahaifiyar Aisha ta wayar tarho, wadda ta nemi a sakaya sunanta
ta ce cutar farfadiya ce ta kama Mu’aruf a lokacin da yake ganawa da mahaifin budurwarsa.

“Shi yaron dama yana da ciwo. Ya nemi yarinyar amma ta ki yarda saboda yana da ciwon farfadiya”.

Ta ce daga baya ya sami mahifin yarinyar, inda ya yi ikirarin “ton musu asiri, domin yarinyar ma
tana dauke da cikinsa.”

Kanwar yarinya ta kara da cewa uban yarinyar ya yi alkwarin kai ‘yarsa asibiti a auna ta ko da
gaske tana da ciki.

Ya kuma ce zai dauki mataki a kan yaron idan har ba ta da ciki.

“Da jin wannan maganar, sai yaron ya yanke jiki ya fadi, har kyaure ya yanke shi”, inji kanwar yarinyar.

Ta kuma bayyana cewa daga baya an kai shi asibiti, inda aka y masa maganin raunin da ya samu.

“Daga baya an sallame shi ya koma
gidansu, amma da daddare kuma sai Allah ya yi mai rasuwa”.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tana gudanar da bincike kan wadanda ake zargi ne don gano ko duka ne ya yi sanadin mutuwar
Mu’aruf Yakubu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar katsina Isah Gambo ya fada wa BBC cewa: “Wadannan mutane na hannunmu muna kuma yin bincike akan dalilan da suka janyo mutuwar saurayin.”

A bincikenta dai rundunar ‘yan sandan katsina ta ce ta hada hannu da hukumomin lafiya da suka yi
gwaji akan ma’aruf kafin a binne gawarsa domin tattabatar da gaskiyar al’aamarin.

©bbchausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.