Sanata kaberu Gay ya fadi Alkiblarsa a 2019

0

Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano mai
wakiltar mazabar sa wanda kuma dan
jam’iyyar APC ya bayyana cikakken goyon bayan sa ga tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Sanata daga Kano ya kware wa Kwankwaso baya, ya goyi bayan tazarcen Buhari Sanatan dai ya bayyana ta cikin nasa ne a lokacin da yake zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa a yau Alhamis bayan gama tattaunawar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Arewaclass ta samu dai cewa Sanata Gaya wanda kuma shugaban kwamitin manyan ayyuaka na majalisar ya bayyana cewa idan Shugaba Buhari ya lashe zaben 2019, zai kammala dukkan manyan ayyukan hanyoyi da sauran su.

Haka nan kuma Sanata Kabiru ya bayyana cewa babban makasudin ziyarar da ya kai wa shugaban kasar shine domin ya gode masa akan zuwan sa Kano a kwanan baya.

©naij

Leave A Reply

Your email address will not be published.