Rahama Sadau ta kai karar Nafisa Abdullahi kotu

9

Jaruma Rahma Sadau ta maka Nafisa Abdullahi a kotu.

wanda tace tana neman hakin ta agun Nafisa Abdullahi, Wanda tace ta hana ta kudin ta har naira dubu tamanin da tara.

Wanda Rahma Sadau taba Nafisa
Abdullahi domin ta fito acikin fim din ta maisuna RARIYA, Amma har aka gama yin fim din Nafisa Abdullahi bata fito koda sau daya acikin fim din ba.

Anayin wannan sharia’a ne akotun Nomans land dake Kano State. Wakiliyar mu ta kotu Sadiya Rk Panshekara ta ruwaito mana
cewa: za’aci gaba da sauraron shar’ar .

Azantawar da wakiliyar mu tayi da wadda akeyin kara Nafisa Abdullahi sai jarumar tace:
“ni ba wasu kudi da Rahma ta bani dan nayi mata fim, Abinda nasani shine, tace tanaso na fito acikin fim din ta maisuna RARIYA nace zan fito amma sabida wasu dalilai ban fito ba, amma ni ba wasu kudi da
ta bani. Inji Nafisa Abdullahi”

To, mu dai aikin mu bibiya za kuma muci gaba da kawo maku yanda shari’ar take tafiya.

©sadikblog

Leave A Reply

Your email address will not be published.