Nigeria zata dauki matasa aiki

0

Gwamnatin Najeriya ta ce a farkon makon gobe
za ta kaddamar da shirinta na samar da ayyukan
sa-kai na koyarwa 500,000 ga ‘yan kasar
wadanda suka kammala karatun jami’a amma ba
su da aiki.
A karkashin tsarin dai za a rika biyan wadannan
matasa albashi yayin da suke aikin koyarwa kafin
su samu aiki.
Wannan shiri dai daya ne daga cikin shirye-
shiryen da gwamnatin Najeriyar ta yi alkawarin
aiwatarwa don inganta rayuwar al’umma kai-
tsaye.
Wata sanarwa da ta fito daga ofisihin mataimakin
shugaban kasar Yemi Osinbajo, ta ce a ranar
Lahadin makon gobe ake sa ran shafin intanet
din da duk mai sha’awa zai je don cike bukatarsa
zai fara aiki, ko da yake tun ranar Asabar za a
bude shafin wanda adireshinsa shi ne
npower.gov.ng.
Sanarwar ta kara da cewa yayin da suke wannan
aikin sa-kai na karantarwa a makarantun
firamare da na sakandare, za a rika biyan
matasan naira 23,000 duk wata .
A jawabin da ya yi na cika shekara guda da
hawansa mulki ne dai Shugaba Muhammadu
Buhari ya sanar da kaddamar da shirin, wanda ya
ce an ware kudin da ake bukata don aiwatar da
shi a kasafin kudin kasar na bana.
Masu suka dai sun jima suna zargin gwamnatin
da gazawa wajen daukar matakan da suka dace
don farfado da tattalin arzikin kasar, da samar da
ayyukan yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.