Nigeria Ta lallasa japan A gasar oliyampic

0
Tawagar kwallon kafar Najeriya bangaren maza ta samu nasara a kan takwararta ta kasar Japan a gasar wasannin motsa-jiki na Olympics a birnin Rio. Tawagar ‘yan wasan Najeriya, Dream Team, ta doke Japan da ci 5-4 a gasar Olympic duk da cewa ba su isa birnin Rio na kasar Brazil da wuri ba, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin ya saba wa ka’ida. A jiya da daddare ne aka yi wasan gabannin bikin bude gasar a hukumance. Idan an jima ne za a gagarumin bikin bude gasar a hukumance. Rahotanni daga birnin Rio da sauran biranen da za a yi wasannin gasar na cewa na dauki tsauraran matakan tsaro. Mahkunta a kasar na fuskantar kalubale daga masu adawa da gasar, wandanda tun jiya Alhamis suka yi zanga-zanga, har wasu daga cikinsu suka yi yunkurin kashe fitilar gasar da ruwa a bokatai

Leave A Reply

Your email address will not be published.