[Na farko] Zakzaky yayi Hira da yqn jarida

3

Zakzaky yayi hira da yan jarida

Shugaban kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da ‘yan Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce ya yi fama da karamin shanyewar jiki a cikin makon jiya.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko ranar Asabar tun bayan da aka kama shi fiye da shekara biyu da
suka wuce.

Malamin addinin ya bayyana ne a Abuja tare da maidakinsa Zeenah wadda ake tsare da su tare.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a Zaria da ke jihar Kaduna, bayan sojoji sun
yi wa gidansa kawanya.

Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria fitar na dauke da hotunan Malamin a lokacin da yake jawabi ga ‘yan jaridar.

Gidan talbijin na Channels ya ambato Sheikh El- Zakzaky na cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa
lau.

Ya kuma gode wa ‘yan Najeriya saboda addu’o’in da suke yi masa.

A makon nan ne dai aka yi jitar-jitar cewa malamin ya rasu.

Ga yadda ganawarsa ta kasance da ‘yan jarida:

‘Yan jarida: Barka da rana?

‘Yan jarida: Ko za ka iya ganawa da mu?

Sheikh El-Zakzaky: Idan sun amince kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha)

Sheikh Zakzaky: Wane hali kake ciki?

‘ Sheikh Zakzaky: Na samu shanyewar barin jiki a ranar Juma’a 5 ga watan Janairun bana

Sheikh Zakzaky: Jikin ya yi tsanani ranar Litinin, amma daga baya jikin ya yi sauki

‘Yan jarida: Yaya kake ji yanzu haka?

Sheik El-Zakzaky: Ina samun sauki jami’an tsaro sun bari na gana da likitan.

Ina godiya ga Allah. Ina samun sauki.

‘Yan jarida: Kana da wani abu da za ka kara cewa.

Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya ga addu’o’inku.

‘Yan jarida: Mun gode

Sheikh El-Zakzaky: Na gode.

Zakzaky ya shafe fiye da shekara biyu a hannun gwamnatin Najeriya
Sau da dama kotunan kasar suna bayar da umarni ga gwamnatin Najeriya ta saki Malamin, sai dai ba ta yi hakan ba.

Mabiya Malamin sun gudanar da jerin zanga-zanga da zummar matsa lamba ga gwamnatin ta
sake shi.

Sun yi zargin cewa ana tsare da shi ba bisa ka’ida ba, ko da yake ministan shari’ar kasar

Abubakar Malami ya shaida wa BBC kwanakin baya cewa suna ci gaba da tsare shi ne saboda sun daukaka kara a kan umarnin da kotunan suka
bayar.

Source: bbchausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.