Maryam booth ta nuna fiskar Sabon saurayin ta

210

RANAR 28 ga Yuni, 2020 jarumar Kannywood Maryam Booth ta wallafa hotunan wani matashi tare da bayyana shi a matsayin sabon masoyin ta. Ta bayyana cewa sunan sa Muhammed Asad Anthony Odozi.

My love, having you in my life is like having all the riches of this world. I will treasure you until the day my life on this planet is up. Have yourself a heavenly birthday. Dim oma muhammed asad anthony odozi @valor347.”

 Mujallar Fim ta fassara waɗannan kalamai kamar haka: “Masoyi na, kasancewar ka a rayuwa ta tamkar samun dukkan arzikin da ke cikin duniyar nan ne. Zan riƙe ka da daraja har zuwa rana ta ta ƙarshe a doron ƙasa. Da fatan za ka more wannan lokaci na zagayowar ranar haihuwar ka. Dim oma muhammed asad anthony odozi @valor347.” Maryam ta tura wannan saƙon tare da hotuna uku na shi Muhammed ɗin.

 Ganin wannan saƙon, mutane da dama da ke bin jarumar a shafin ta na Instagram sun yi mata caa, su na taya ta murnar samun sabon saurayi tare da taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Wasu daga cikin makusantan Maryam na zahiri sun kira shi da “angon mu,” wanda hakan na nuni da cewar da ma can sun san da maganar, kuma sun yi na’am da ita. Akwai kuma waɗanda su ka yi wa Maryam tambaya. Misali, wani ya tambaye ta shin Musulmi ne shi wannan Odozi ɗin? Ta yiwu saboda ganin kalmar ‘Anthony’ a cikin sunan sa ne.

 A kan wannan tambayar, ɗaya daga cikin makusantan Maryam, wato Badariyya Ƙalarawi ta BBC Hausa, ta ce wa mai tambayar: “Saboda Allah ina ruwan ka?” Ita kuma Maryam sai ta ce wa Badariyyar: “Aunty B., don Allah ƙyale shi. Idan mutum ba Bahaushe ba ne, shi kenan ba Musulmi ba ne gurin wasu.”

 Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin samun samun ƙarin bayani game da wannan soyayya ta Maryam Booth da Muhammed Odozi, amma abin ya ci tura. Wakilin mu ya kira ta a waya ya fi sau shurin masaƙi, amma ba ta amsa ba. Kuma ya tura mata da saƙon tes, ya ce mata ya na so su yi magana kan batun auren ta da ake cewa ya kusa, shi ma ba ta ce komai ba. Hasali ma dai, daga baya sai ta je ta cire saƙon tare da hotunan daga shafin ta. Mun dai ga alamar cewa an san da zaman Muhammed Odozi a gidan su Maryam, domin kuwa fitaccen mawaƙi kuma jarumi, Yakubu Muhammad, shi ma ya taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa tare da kiran sa surukin sa. 

Yakubu, wanda ya taɓa auren Sadiya yayar Maryam har sun haifi ‘ya guda ɗaya, ya rubuta a shafin sa na Instagram: “Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwar ka. Ɗan’uwa na, aboki na, suruki na. Da fatan za ka more wannan ranar.” 

Da alama dai Maryam da Muhammed sun shaƙu matuƙa, domin ko daga hotunan sa da ta tura a shafukan ta na TikTok da Instagram za a iya fahimtar haka. Hotuna ne da aka ɗauka a lokuta daban-daban, kuma su na nuno masoyan biyu a wurare daban-daban da shiga daban-daban.

Akwai ma hotunan da su ka ɗauka a cikin jirgin sama, wanda hakan ya nuna cewa sun ɗauke su ne a watannin baya kafin a hana zirga-zirgar jiragen sama a watan Maris saboda cutar korona. 

Ita dai Maryam Booth, ta sha gwagwarmayar soyayya da manema daban-daban masu cewa za su aure ta, amma a ƙarshe sai maganar ta shiririce.

Amma wannan shi ne karo na farko da ta bayyana soyayya ƙarara ga wani mutum har ta sadaukar da rayuwar ta gaba ɗaya gare shi a idon duniya. 

Idan kun tuna, a farkon wannan shekarar an yi terere kan wani guntun bidiyo mai nuno Maryam tsirara futuk da ya ɓulla a soshiyal midiya. 

Maryam ta zargi mawaƙi Deezell da fitar da bidiyon, wanda aka ɗauka da waya, to amma ya musanta zargin. 

A ƙarshe, su ka maka juna a kotu, kowannen su ya na so a bi masa haƙƙin sa kan ɓatanci da tozarci a idon duniya.

 Al’amarin ya baƙanta wa tsoffin masoyan biyu rai matuƙa. Mai yiwuwa Maryam za ta samu sa’ida ta hanyar sabon saurayin ta, wato Muhammed Asad Anthony Odozi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.