Khadija Kyari tasha Da kyar a Hadarin mota

135

Jaeumar fim ɗin Hausa, Khadija Kyari, ta tsallake rijiya da baya yayin wani haɗarin mota da ya ritsa da ita a hanyar Katsina. 

Haɗarin ya Faru ne a Ranar Alhamis, 2 ga Yuli, 2020 a kusa da garin Kankiya dake Jihar Katsina, lokacin da su ke kan hanyar su ta zuwa Kano. 

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa Khadija da wasu ‘yan gidan su sun je biki ƙasar Nijar ne, su na kan hanyar su ta komawa gida Kano sai motar hayar da su ke ciki ta ƙwace ta runtuma cikin daji da su ta faɗi.

 Khadija ta ji muggan raunuka, musamman a fuskar ta da hannun ta. Mun kira wayar kyakkyawar jarumar ta Kannywood domin jajanta mata da kuma samun ƙarin bayani kan wannan haɗari, amma ba ta amsa ba. 

Majiyar mu ta ce: “Gaskiya ba ta iya magana.

Wayar ma babar ta ce ta ke ɗagawa, wani lokacin yayar ta.

 “An mata ɗinki ne a bakin ta da karan hancin ta, sannan kuma da tsagewar ƙashi a hannun ta na dama.” 

Majiyar ta ƙara da faɗa wa mujallar Fim cewa sauran mutanen da ke cikin motar ma “duk sun kakkarye; ita ce ma nata abin ya tsaya iya haka.”

Yan bikin sun haɗa da wasu ‘yan’uwan ta biyu mata da wata ƙawar ta mai suna Ummi.

 ‘Yan fim da dama sun je sun gaida jarumar a gidan su da ke unguwar Ladanai Ringroad Bypass, Kano. 

Khadija Kyari ta fito a finafinai da dama, waɗanda su ka haɗa da ‘Hafiz’, ‘Lantana,’ da sauran su. 

Da fatan Allah ya ba ta lafiya, kuma ya tsare gaba, ya tsare mu da sharin karfe Ameen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.