Kasan Wane jarumai ne sukayi ficce a 2017

0
An kawo sunayen su ne bisa irin rawan
da suka taka a farfajiyar Kannywood

A cikin akwai Zango, Ali Nuhu, Rahma
Sadau da sauran su, A lokacin da muka gabato karshen shekara 2017,

arewaclass.com.ng ta kawo muku jerin sunayen jaruman Kanywood da aka fi jin
su a cikin wannan shekara.
Adam A Zango
Adam Zango yana daga
cikin yan wasan da suka fi shanawa a
fina-finan Kannywood a cikin shekara
2017, kuma Adamu yayi matukar burgewa wajen rera wakoki da rawa.

Bayan haka Adamu ya fito aka kafofin sada zumunta ya koka akan yadda wasu ke   masa zagon kasa a harkar sa, kuma yayi alkwarin takawa duk wanda yake neman sa da rigima birki.
Rahama Sadau
Idan ana maganar yin sharihi ne a Kannywood tabbas sai suna Rahama ya fito, Rahama jaruma kuma tauraruwa ce dake shanawa a farfajiyar fina-finai, ba Hausa kadai ba har da na turanci.

Rahama ta daya daga cikin yan
wasa da aka ji su a cikin wannan shekara.
Ummah Shehu
A cikin wannan shekara  ba a bar Ummah a baya ba, Ummah Shehu ta kara yin suna a farfajiyar Kannywood bayan katobarar da tayi akan tambayoyi da aka mata dangane da addini.

Umma ta shiga tsaka mai wuya inda mutane suka ta sukar akan rashin iya amsa tambayoyi  game da addinin musulunci.

Ali Nuhu
Ali Nuhu wanda aka fi sani da
sarki baya bukatar doguwar bayyanai akan sa, saboda Sarki Ali Nuhu bashi da na biyu a Kannywood.
A cikin wannan shekara sarki ya anshi kyautar giramawa a kasar Birtaniya.

Sadiq Sani Sadiq
Idan dai shiri na  bukatar jarumi da ya kware, ka nemi Sadiq.
A 2017 Sadiq yayi abun yabo.
Daga wasu shiri da basu kai ga zuwa fitowa ba  kamar su dan Iya, Gimbiya sailuba da sauran su, Sadiq ya nuna kwarewar sa matuka.
Nafisa Abdullahi
Nafisa, kyakkyawaryarinyar son kowa kin wanda ya rasa.
A shekarar 2017 Nafisa ta dawo daga hutun sannan ta koma harkar fim. Idan dai ana maganar saka hoto a Instagram to Nafisa  ta daga tuta wannan fannin.
Fati Washa

Fati Washa ta na daga cikin yan wasan da suka shana a wannan shekara.
Akwai manyan finafinai da aka
tallata su a wannan shekara inda wasunsu ma har sun fito.
Maryam Yahaya

Maryam Yahaya itace Karama amma kuma mai gallaza wa manya azaba.
Idan baka gane ba kalli fim din Mijin yarinya. 
Duk da dai sabuwar fitowa ce a harkar finafinai ta na shanawa a farfajiyar finafinan Hausa.

©naij

Leave A Reply

Your email address will not be published.