[Kannywood] Na amince zan Auri sheik Datti Assalafi

19

Fitacciyar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa Fati Muhammad ta mayarwa da Ustaz din ya yi mata korafin biyewa masu kudi yan siyasa suna kwana dasu a hotel mai suna Datti Assalafiy martani a wani wasikar da ta rubuta.

Wasikar Fati Ga Malam Datti Assalafiy.

Tace;

“Na ga rubutunka akaina kuma nagode duk da dai ka bani mamaki a matsayinka na wanda kake kallon kanka Ustazu amma maimakon
kayi amfani da iliminka ka yi min nasiha sai ka bi son ranka, har kake fadin muna biyewa Masu Kudi da ‘Yan Siyasa Suna kwana damu a
Hotel Suna diban kudin Talakawa Su Bamu.

Idan nasiha zaka yi ka yi yadda ake yinta, nasan inda ace kanwarka ce ko ‘yarka ba zaka fadi mata wadannan munanan kalaman ba da
sunan Wa’azi amma idan cin mutumci ne yasa kayi wannan Rubutun to ina jiran ci gabansa,
Kuma tunda Kace na tuba na nemi miji na aura to a shirye nake zan aureka in dai har don Allah kake wannan Wa’azin naka.”

Bissalam

Leave A Reply

Your email address will not be published.