Cushe a kasafin kudi: “Ba ma tsoron binciken EFCC”

0

Shugabannin majalisar wakilan Najeriya sun ce ba sa
wata fargabar binciken da hukumar EFCC mai yaki da
masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati za ta yi a kan
zargin yin cushe a kasafin kudinshekarar 2016.
Mai tsawatarwa na majalisar, Alhassan Ado Doguwa
ya shaida wa BBC ya ce ba su ci nanin ba don haka
nanin ba za ta ci su ba.
A cewarsa doka ce ta kafa hukumar EFCC, don tana da
ikon gudanar da binciken, yana mai cewa a shirye
yake ya amsa dukkan tambayoyin da za a yi masa
game da kasafin kudin.
Sai dai ya musanta cewa sun yi cushen kudade a
kasafin kudin na bana, kamar yadda tsohon shugaban
kwamitin kasafin kudin Abdulmumini Jibrin ke zargin
su da aikatawa.
Shi dai Jibrin ya zargi shugaban majalisar Yakubu
Dogara da Alhassan Ado Doguwa da wasu manyan
‘yan majalisar da yunkurin yin cushen sama da N70bn
a kasafin kudin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.