Buhari ya nada matattu a Gwamnatin sa Mukami

1

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da sunayen mutanen da ta nada su shugabanci a wasu ma’aikatun gwamnati.

Amma abin mamaki sai kawai aka ga
sunayen wasu matattun ‘yan Najeriya a cikin wadanda aka nadan.

Gwamnatin ta nada mutum 209 da mambobi fiye da 1,250 domin su jagoranci hukumomin.

Al’amarin ya zama baban abin mamaki ga yan Najeriya, musamman a shafukan sada zumunta.

Amma Garba Shehu, wanda shi ne kakakin shugaban kasa ya kare gwamnati daga zargin rashin iya aiki.

Ya fada wa BBC cewa an shirya wannan jerin sunayen ne fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Ya kuma bayyana cewa, “Tun watan Oktobar shekarar 2016 aka rubuta sunayen.

Amma sai aka ajiye shi domin sukar da wasu gwamnoni suka yi.”

Da alama babu wanda ya tantance jerin
sunayen kafin aka wallafa shi ranar Jumma’a.

Kakakin gwamnatin bai ga dalilin da za a
dauki matakin ladabtarwa akan wadanda
suka saki sunayen ba.

“Babu wani dalilin da za a dauki mataki akan wani jami’in gwamnati saboda wannan kuskuren,” inji shi.

A cikin sunayen akwai sunan sanata Francis Okpozo wanda ya mutu a watan Disambar 2016, amma sai ga sunansa a cikin nadaddun.

An nada shi ya shugabanci hukumar Nigeria Press Council.

Ban da shi akwai Donald Ugbaja, wani tsohon mataimakin sufeto-janar na ‘yan sandan Najeriya wanda ya mutu a farkon wannan shekarar, wanda aka nada shi domin ya shugabanci hukumar Consumer Protection Council.

Akwai kuma marigayi Rabran Christopher
Utov, wanda sunansa ya fito a jerin sunayen mambobin hukumar Nigeria Institute of Social and Economic Research.

Garba Shehu ya ce za a sauya sunayen
matattun mutanen da na wasu ‘yan kasar da suka cancanta.

©bbc

Leave A Reply

Your email address will not be published.