Babu wani abu da yake da wahala a Waka

18

Fitaccen jarumi kuma mawakin wasan barkwanci Ado gwanja yacce babu wani abu dake da wahala a rera waka, inda yacce ya yi waka akalla 600 kuma duk da ka ya rera su.

Ado Gwanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da Shafin BBC Hausa Instagram Live ranar Alhamis.

Da aka tambaye shi ko yin waka yana da wahala, sai ya ce “gaskiya babu abin da yake ba ni wahala” idan ya zo rera waka.

kaza, ko yanayi kaza’, sai a yi min kida sikeleton…ina cikin ji wakar za ta zo. Idan ta zo sai na ce ‘samo min furodusoshi,” a cewar Ado Gwanja.

Ado Gwanja ya ce cikin kusan waka dari shida da ya yi, wakoki ba su wuce biyu ba wadanda ya zauna ya rubuta saboda wasu sun ba shi shawarar yin hakan.

Ya ce wakar da ya soma yi ita ce Gawasa “kuma da na yi ta ni kadai aka bari na yi ta jin kaya ta. Na ji kayata ta ishe ni, na kuna mnata inda na ajiye ta”.

Wakokinsa da dama sun yi tashe musamman Kujerar Tsakar Gida, Asha Rawa, da Salon Kida.

Mawakin ya ce baya ga sana’ar waka, babu sana’ar da yake so kamar ta shayi.

“Saboda mu asali a gidanmu – ko mace ko namiji, har iyayenmu da sana’ar shayi aka auro su,’ in ji Ado Gwanja.

Ado Gwanja ya ce ya daina fitowa a matsayin dan daudu a fina-finan Kanyywood saboda “na fi so matata ta dan yi dariyarta ta fadi ta tashi daga ni sai ita.”

A baya dai ya shaida wa BBC Hausa cewa tsabar yadda ya iya kwaikwayon ‘yan daudu ne ya sa ake sa shi a fim din da ya danganci haka.

Wannen mawaki Ado Gwanja

  • Dan asalin unguwar Kofar Wambai ce ta Kano
  • Mahaifinsa shahararren mai shayi ne da ak fi sani da Gadagi Mai Shayi
  • Ya yi karatu har zuwa sakandare
  • Yana da mace daya da ‘ya daya
  • Ya kan fito a fim kuma yana waka

Leave A Reply

Your email address will not be published.