Ba Mu yarda da gafartawa Rahama Sadau ba

1

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa (MOPPAN), Alhaji Kabiru Mai
Kaba ya ce ba su yarda da matakin gafartawa Rahama Sadau wanda hukumar tace fina-finan jihar Kano ta yi a makon jiya.

Mai Kaba ya mayar da martani ne ga shugaban hukumar tace fina-finai Isma’ila Na’abba Afakalla.

A ranar Talata ne Afakalla, ya shaida wa BBC cewa, a shirye suke su fara tace fina-finan da jarumar za ta rika fitowa a cikinsu da kuma wadanda take daukar nauyinsu.

A watan oktoban da ya gabata ne
shahararriyar jarumar ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da tayi a wani bidiyon waka tana ” Rungumar ” wani mawakin hausa Hip Hop wato ” Classiq “.

©arewablog

Leave A Reply

Your email address will not be published.