Apc ta ja kunnen Abdulmumini jibrin

0
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi tsohon shuagaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilan kasar, da ya daina maganganu a kafafen yada labarai kan rikin majalisar. Jam’iyyar ta nemi Abdulmumini Jibrin, wanda ke wakiltar Bebeji da Kiru a jihar Kano, da kada ya kara cewa komai game da rikicin a kafafen yada labarai da kuma shafukan sada zumunta. Shi dai dan majalisar ya wallafa wasu bayanai, sannan ya rinka hira da kafafen yada labarai, inda ya ke zargin shugabannin majalisar da almundahana a kasafin kudin kasar. Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga mukamin shugaban kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa. *. Rikici ya barke a majalisar wakilan Nigeria *. Al’amura na kara dagulewa a majalisar wakilan Najeriya A wata wasika da shugaban APC mai kula da shiyyar Arewa, Senata Lawal Shu’aibu ya aikewa dan majalisar, ya yabawa Mista Jibrin game da amsa gayyatar jam’iyyar da ya yi ranar Talata. Sai dai ya ce jam’iyyar ta ba ta ji dadin abin da ke faruwa a majalisar ba kan badakalar kasafin kudin. Kafin jam’iyyar ta gana da Mista Jibrin, sai da ta tattauna da Kakakin Majalisar Yakubu Dogara, a wani yunkuri na shawo kan lamarin. A baya dai, dan majalisar wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a jihar Kano, yana daya daga cikin na hannun damar shugaban majalisar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.