Aminu momo bai isa ya kure ni ba

1

Jarumi Bello Muhd Bello wanda akeyiwa lakabi da General BMB, yasha alwashi akan jarumi kuma ma’aikaci agidan Arewa24 television Aminu Momoh.

Dalilin wannan alwashi da BMB ya yi shine, Aminu Momoh ya gudanar da wani shiri agidan Talabishin na Arewa wanda yake tattaunawa da jaruman kannywood, wanda duk kusan jaruman da ya gayya sai ya
kunyata su gamida qure su idanun duniya.

Mu dauki misali akan jaruma Umma Shehu, ya gayyace ta amma ya katsa ta a idanun
duniya.

Ganin wannan ne ko kuma wata
daban ne yasa BMB yake so a hada shi hira da Momoh ko kuma da akwai wata tsakani, oho.

Ga dai abinda BMB yace;

“Inaso a hada ni hira da Momoh domin nine maganin sa.

Duk abinda yake takama da shi
nafi shi, Yanda ya qure wasu ko ya katsa wasu jarumai ni sai dai reshe ya juye da mujiya.

Shi kan sa yasan haka domin na kira shi awaya dan sanar da shi burina na yin hira da shi amma har yanzu shiru no replied.

Wannan ya tabbatar min cewa ya karaya da ni.

Har gobe inaso a hada ni hira da Momoh. Har yanzu ina chigaba da cewa: ”A  hada ni hira da Momoh nine maganin sa”.

©sadikblog

Leave A Reply

Your email address will not be published.