Alamomin da zasu ganar da ke cewa na miji zinayake so yayi da ke

139

Kamar yadda abun ya riga ya zama ruwan dare,yanmata da yawwa kan fadacikin tarkon samarin shaho savoda karancin fahimtar abubuwqn da zamubayyana a kasa.

Ku dubu wadannan abubuwan da kyau kuma ku kalke so somin idan kukaga haka a tareda wanda kike soyayya daahi to zina yake son yi dake:

  • 1: Zaki ga cewa bai yabon halayenki ko dabi’unki masu kyau kullum maganan halittun jikinki yafi magana maimakon wasu halayenki.
  • 2: Bazai miki maganan aure ba kuma idan kin masa bai daukan zancen da mahimmanci.
  • 3: Yana gudun ‘yan uwanki danashi su ganki. Don haka da wuya yagabatar dake a wajen wasu na kusa dake kuma zai rika kaucemiki idan kika bukaci yaga wasu naki nan ma zai rika zullewa.
  • 4: Mafiyawan lokaci yafison ki ziyarceshi maimakon shi ya rika zuwa wajenda kika.
  • 5: Yana son gayyatarki wuraren shakatawa da holewa maimakon wajen da zaki samu karuwa na addini ko na wani illimin zamani.
  • 6: Wasu alamun shine idan kikayi wani kuskure baya iya fitowa a fili ya nuna miki saboda babu son gaskiya a zuciyarsa kada ranki.
  • 7: A duk lokacin da kuka kadaita burinsa shine ya tabaki ko ya jawoki a jikinsa.
  • 8: Sakonninsa na waya zantukan batsa da yabon halittarki sunfi yawa maimakon wasu maganganu da zai miki masu mahimmanci.
  •  9: Duk hiran da zaku yi da wuya ya rika zuwa miki da zantunka da zai amfani rayuwanki. Ko hira yadda zai taimaki rayuwanki.
  • 10: Bai damuwa da kokarin saninki, tarihin ki dana zuri’arku. Ko sanin abubuwan da kike burin yi ko zama.

Wadannan sune wasu daga cikin alamun da zaki iya fahimtar saurayin namiji mai sha’awan zina dake ba aure ba.


Da fatan idanuwaku zasu bude ku iya gane masu sonku na gaskiya, Qllah yasa mu da ce sannan kuma mu fahimta cikin sauri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.