Abin da yasa na ziyarci Buhari jonathon

1
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci shugaban kasa Buhari a jiya Laraba bayan da suka gama tattaunawar su a fadar gwamnati. Yayin da yake magana da manema labarai, Jonathan ya ce ya ziyarci shugaban kasar ne domin ya kawo masa rahotanni akan al’amuran da yake ciki a kasashen waje. Ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon shugaban kasa, ya zama mallakar kasa, kuma hakan ya dora masa wasu nauye nauye da dole ne ya sauke. Ya ce yawancin ayyukan da yake yi a kasashen waje sun kunshi bayyana a gaban jama’a, adon haka sun shafi kasar. Ya bayar da misalin aikin da aka basa na shugabantar tawagar kungiyar tarayyar Afrika da za su kula da zaben kasar Zambia. Saboda haka ne ya kan ziyarci shugaban kasan lokaci zuwa lokaci ya kawo masa rahotannin wadannan ayyuka. Ya ce wani lokacin da daddare ma yake zuwa, babu mai ganinsa. Ya ce yin hakan al’ada ce ta gwamnatin Nijeriya. Ga me da fitinar da ke faruwa a yankin Niger Delta, Jonathan ya ce sam bai yarda da wani abu ba da zai iya kawo rabewar kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.