Abin da yasa baa gani na a Fim yanzu

132

An shafe dogon lokacin ba a ji ɗuriyar fitacciyar jaruma Zulaihat Ibrahim (Zeepreety) a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood ba.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen shirin fim na Kannywood.

 Jarumar ta kasance mai alamar rawar kan da in dai ta na waje, to ba ta ɓuya, amma sai ya zama an daɗe ba a jin ta ko ganin ta a cikin masana’antar; ba ma gani na ido da ido kaɗai ba, hatta a shafukan ta na soshiyal midiya ma ba a ganin ta.

Zpreety na cikin jaruman da su ka fi kowa yin bidiyon kan su, su na turawa a Instagram da sauran shafuka.

 Labarin da ake ta yaɗawa tun wajen watanni biyar da su ka gabata shi ne Zpreety ta samu kan ta a cikin wani mawuyacin hali ne na rashin lafiya, wanda har ta kai ga ta koma garin su, wato Zuru a Jihar Kebbi. 

Abin da ya ƙara tabbatar da maganar rashin lafiyar tata shi ne yadda aka daina samun ta a waya, domin duk wani makusancin ta a industiri idan wakilan mujallar Fim su ka tambaye shi abin da zai faɗa masu shi ne ba ya da wani labari game da ita, abin da ya sani dai shi ne ya dai ji an ce ba ta da lafiya. Kwatsam, a ‘yan kwanakin nan sai aka fara ganin Zpreety ta na ɗan tura saƙwanni a soshiyal midiya.

Hakan ya alamta cewa jarumar ta samu sauƙi. Wakilin mujallar Fim ya jima ya na ta kiran wayar ta, amma ya na samun ta a kashe.

Sai a ranar Lahadi, 11 ga Mayu, 2020 bayan sallar magariba ya gwada kiran ta, inda ya yi sa’ar samun ta. A taƙaitacciyar zantawar da su ka yi, Zulaihat ta tabbatar wa da wakilin mu cewa lallai ta daɗe ta na fama da rashin lafiya.

 A cewar ta, “Gaskiya ne na yi rashin lafiya na tsawon lokaci, shi ya sa ma ba na samun ɗaga waya domin ban san wanda zai kira ni ba, kuma ina cikin wani hali ne a lokacin.

 “Amma dai a yanzu na samu sauƙi tunda ga shi yanzu mu na yin magana da kai. “Kuma duk wasu abubuwa da ba na iya yin su, a yanzu ina yi.

Don haka na samu sauƙin jiki na.” Da mujallar Fim ta yi mata maganar raɗe-raɗin da ake yi cewa wai an yi mata asiri ne, wanda shi ne dalilin rashin lafiyar tata, sai ta ce, “Ai na zata ka kira ni ne don mu gaisa ba don neman labari ba.

Don haka in don wannan ne, ka bari nan gaba zan kira ka mu yi maganar.” Mun ƙara tambayar ta tunda ta samu sauƙi, to ta dawo Kano ne a yanzu? Sai ta ce, “Ai yanzu ana zaman gida ne, don haka ina garin mu da zama, sai dai in gari ya yi lafiya zan dawo.”

 Maganar da Zulaihat Ibrahim ta yi kenan a karon farko bayan ta samu lafiya daga doguwar rashin lafiyar da ta sha fama da ita.  Mu na fatan Allah ya ba ta cikakkiyar lafiya, kuma ya kiyaye gaba, amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.