Bangan Anfanin nuna Hotunan da akayiwa fyade b

19

RUƘAYYA Umar Santa wacce aka fi sani da Dawayya ta yi roko ga jama’a da su daina sanya fuskokin yaran da iftillain fyaɗe ya fadawa safukan sada zumunta don kada a rinƙa ƙyamar su.

 Fitacciyar jarumar Kannywood ta ce sanaya hotunan tonan silili ne.

 A wata tattaunawa da da kamfanin dillancin labarai na kasa (wato News  Agency of Nigeria, NAN) ya yi da ita a Kano ran Talata, Dawayya ta bayana cewa a wasu daga cikin bidiyoyin da ake yaɗa a shafukan na sada zumunta cikin ‘yan kwanakin nan an nuno fuskokin iyayen yaran da aka yi wa fyaɗen.

 Ta kara da cewa, “Ni ban san abin da doka ta ce a kan hakan ba, to amma abin bacin rai ne domin hakan zai iya sa a riƙa ƙyamar yaran da abin ya shafa. “Na ga yarinya ‘yar shekara uku ana yi mata fyaɗe, kuma aka nuno mahaifiyar ta ana yi mata tambayoyi a kan al’amarin a wani guntun bidiyo.

Na tabbatar wannan ƙaramar yarinyar ba za ta so haka ba idan ta girma.”

 Jarumar, wadda kuma furodusa ce, ta yi kira ga iyaye da su yi ƙoƙarin kare mutunci da martabar ‘ya’yan su. 

Bugu da ƙari, ta yi kira ga iyaye maza da su taya matan su aikin tarbiyyantar da ‘ya’yan su tare da tsare su. Kamfanin dillancin labaran ya ce an yaɗa wasu bidiyoyi a soshiyal midiya inda ake nuno ƙananan yara ana yi masu fyaɗe, kuma hakan bai yi wa mata da yawa daɗi ba.  

Mujallar Fim kuma ta ruwaito cewa Ruƙayya Dawayya ta yi wani faifan bidiyo a Instagram inda ta ƙara yin Allah-wadai da yadda ake fallasa matan da aka yi wa fyaɗe. 

Dawayya, wadda ta ce ta yi wannan bidiyo ne a “cikin tsananin ɓacin rai,” ta ce, “Don me don an yi ma yarinya fyaɗe sai ku zo ku saka su a soshiyal midiya? Ba daidai ba ne.

Kun tozarta su.” Ta ce hatta nuno dattijai maza da su ka aikata laifin fyaɗen tsirara da ake yi a bidiyo bai dace ba. 

“Wani hau ne. Wani bai san abin da ya sa ya aikata wannan ba,” inji ta. 

Ruƙayya Dawayya a cikin bidiyon da ta yi kan al’amarin Dawayya ta ƙara da cewa su ma masu ɗaukar irin waɗannan bidiyoyin su na ɗorawa a shafukan su na soshiyal midiya, ba su kyauta ba. “Idan ‘ya’yan ku aka yi wa hakan, za ku ji daɗi?” inji ta. A cewar ta, yin hakan yaɗa baɗala ne kuma hakan ya fi aikata baɗalar laifi. “In mutum ya aikata laifi, a kai shi a hukunta shi mana,” inji ta. Zaune a cikin mota, kuma ta na riƙe da tasbahar latsawa, jarumar ta yi nuni da cewa ‘yan Arewa ne ma ke yin irin wannan ɗabi’ar ta fallasa yaran da aka yi wa fyaɗe, su ko ‘yan kudu ba su yin haka duk da yake ana aikata irin wannan mugun alkaba’in a kudu ɗin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.